Hukumomi a birnin Bangkok sun kama wata budurwa ‘yar shekara 19 ‘yar ƙasar Taiwan bisa zargin safarar kunkuru guda 30 masu kariya.

An cafke budurwar ne a filin jirgin saman Suvarnabhumi yayin da take shirin hawa jirgi zuwa birnin Taipei dake kasar Taiwan.

Hukumar kula da namun daji ta Thailand ta ce jami’anta sun fara zargin ta ne bayan sun lura da motsinta da ba su gamsu da shi ba a sashen masu tashi.

Bincike ya gano cewa ta ɓoye kunkuru guda 30 a jikinta, inda guda 29 ke da rai, yayin da guda ɗaya ya mutu.

Rahotanni sun ce ta ɗaure kunkurun da tef domin hana su motsi, ta saka su cikin jakunkuna na yadi, sannan ta manne su a jikinta domin kauce wa ganowa.

An bayyana cewa kunkurun nau’in Indian star tortoise na daga cikin dabbobin da ake matuƙar karewa, kuma suna fuskantar barazanar ƙarewa saboda yawan buƙatarsu a kasuwar haramtacciya, musamman a matsayin dabbobin ado.

Thailand na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba a nahiyar Asiya.

Hukumar kwastam ta kiyasta darajar kunkurun da aka kama da kusan dala dubu 9 a kasuwar bayan fage.

An gurfanar da budurwar bisa laifin safarar dabbobi masu kariya da kuma ƙoƙarin kauce wa dokokin kwastam.

Hukumomi sun ce bincike na ci gaba domin gano ko tana da alaƙa da wata babbar ƙungiyar safarar namun daji ta ƙasa da ƙasa.

A halin yanzu, an miƙa kunkurun da suka tsira ga jami’an kula da namun daji domin kula da su, tare da amfani da su a matsayin hujja a shari’ar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version