Alhazan Jihar Kano da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a Kasar Saudiyya sun bayyana gamsuwa da irin kulawar da ake basu a Mina, musamman ta fuskar abinci da kuma harkokin lafiya yayin da aka fara manyan ayyukan Hajji.
Kimanin Alhazai 3,620 daga Jihar Kano ne ke cikin miliyoyin Musulman duniya da ke gudanar da aikin Hajjin bana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Tawagar Yada Labarai ta Ayyukan Hajjin Kano 2026, Mustapha Muhammad, ya fitar.
Rahotanni daga Mina sun nuna cewa Alhazan Kano na samun wadataccen abinci mai gina jiki tun bayan isowarsu, lamarin da ya sanya da dama daga cikinsu bayyana jin dadi da kwanciyar hankali yayin gudanar da ibadunsu.
A wata ziyara da aka kai dakin girki da ake hada abincin Alhazan, an tarar masu girki suna aikin hada abincin rana wanda ya kunshi shinkafa, kaza, lemun sha, ruwa da kuma ‘ya’yan itatuwa.
Haka kuma an tanadi wuraren rabon shayi da kofi da ke aiki tun daga safe har zuwa yamma, yayin da aka cika firij-firij da ruwan sanyi da nau’ikan lemun sha domin Alhazai su rika amfani da su kyauta a duk lokacin da suke bukata.
A bangaren kula da lafiya kuwa, ma’aikatan lafiya da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta girke a Mina na ci gaba da duba lafiyar Alhazai tare da bayar da kulawar gaggawa ga masu bukata.
Hakazalika, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya kai ziyara tantunan Alhazan domin duba yanayin da suke ciki tare da sauraron koke-kokensu domin magance duk wata matsala cikin gaggawa.
Shaidu sun bayyana cewa Darakta Janar din na yawan tambayar Alhazai ko suna fuskantar wata matsala yayin da yake zagayawa tsakanin tantuna da wuraren ibada.
Wannan kulawa da tsare-tsaren da aka shimfida sun taimaka wajen sanya Alhazan Kano cikin walwala da jin dadin gudanar da ibadunsu a Mina.
Lamarin ya kara bayyana kokarin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen tabbatar da jin dadi da walwalar Alhazan jihar a aikin Hajjin bana.
