Daga Ibrahim Sani Madabo

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta nuna rashin amincewarta da ƙarin kashi 50 cikin 100 na kiran waya da Data ga yan Najeriya.

Shugaban Kungiyar NLC,ta Najeriya Joe Ajaero, wanda yayi watsi da karin ya bayyana matakin a matsayin wata hanya ta cutar da ’yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa.

Da yake magana a Abuja, Ajaero ya soki gwamnati da kamfanonin sadarwa saboda fifita samun riba a kan jin daɗin al’umma.

Ya ce ƙarin zai sa harkokin sadarwa su zama masu tsada, inda ma’aikata masu karɓar mafi ƙarancin albashi za su riƙa kashe kaso 15 cikin dari na kuɗin da suke samu a duk wata kan sadarwa.

NLC ta buƙaci a dakatar da ƙarin nan take, tare da yin shawara da masu ruwa da tsaki don sake duba wannan matakin.

Ajaero ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar na iya shiga yajin aiki da kuma ƙauracewa ayyukan sadarwa idan gwamnati ba ta soke ƙarin ba.

Haka ita Kungiyar TUC tayi watsi da karin kiran wayar da Saka Data.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version