Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya cika shekaru 68 a duniya wanda yasa yau, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya tashi murna tare da fatan samun lafiya mai dorewa.

A sakon taya murna da aka fitar, Kwankwaso ya bayyana Dr. Jonathan a matsayin mutum mai kima wanda rawar da ya taka a tarihin Najeriya ta kasance abin alfahari da nuna kishin kasa.

Ya ce matsayin Jonathan a tarihin Najeriya “ba zai gushe ba”, yana mai bayyana shi a matsayin gwarzo mai nuna gaskiya, da sanin ya kamata da jajircewa wajen tabbatar da dimokuradiyya.

Kwankwaso ya kara da cewa yana yi masa fatan karin lafiya, kwarjini da nasara a dukkan al’amuransa.

TST Hausa ta rawaito cewa Kwankwaso ya yi mulkin jihar Kano tare da Jonathan a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version