Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa an samu ƙaruwa a yawan wutar lantarki da ake samarwa a ƙasar, inda ya tashi daga megawatt 3,951 zuwa megawatt 4,300.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Abuja, ta bakin Mai Ba Ministan Wutar Lantarki Shawara na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Hulɗa da Kafafen Yaɗa Labarai, Bolaji Tunji.
Sanarwar ta ce an samu wannan ci gaba ne tsakanin ranar 28 ga watan Maris zuwa 10 ga watan Afrilu, shekarar 2026.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan ƙaruwa na daga cikin ƙoƙarin da take yi na bunƙasa ɓangaren wutar lantarki, tare da magance matsalolin rashin wadatacciyar wuta da ake fama da su a ƙasar.
Ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da zuba jari a fannin makamashi, tare da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, domin ƙara yawan wutar da ake samarwa da kuma inganta rabonta ga al’umma.
Sai dai duk da wannan cigaba, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar katsewar wuta a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ke shafar rayuwar yau da kullum da harkokin kasuwanci.
Masana sun bayyana cewa duk da wannan ƙaruwa da aka samu, har yanzu akwai buƙatar ƙarin zuba jari da gyare-gyare a tsarin wutar lantarki domin a kai ga wadatar da ake buƙata a Najeriya.
