Jigo a Jam’iyar APC a Kano kuma tsohon mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar Dattawan Najeriya Hon. Shehu Isa Direba yi kira ga hukumomi da su rika gudanar da bincike cikin sirri kafin bayyana sunayen mutanen da ake zargi da wasu lamura, domin kare mutunci da kuma guje wa bata suna ba tare da hujja ba.

Kiran ya fito ne yayin da majalisar dokokin Kano ta gayyaci shugaban hukumar ilimin bai daya ta Kano wato SUBEB Alhaji Yusuf Kabir domin binciken zargin sayen takardun daukar aikin koyarwa a hukumar ta SUBEB.

Hon. Direba ya shaidawa TST Hausa cewa kama sunan shugaban na SUBEB zai iya zama bata sunan idan an same shi bashida laifi.

Ya nuna damuwa kan yadda ake gaggawar fito da sunayen mutane a bainar jama’a kafin a kammala cikakken bincike, lamarin da ke iya haifar da rashin adalci da tabarbarewar suna ga wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana cewa wajibi ne a rika bin ka’idojin adalci da bin doka wajen gudanar da bincike, tare da tabbatar da cewa duk wani hukunci ko zargi yana dogara ne kan tabbatattun hujjoji.

Haka kuma, an jaddada cewa manyan jami’an gwamnati da masu rike da mukamai a jihar suna da martaba da kima da ya kamata a kiyaye har sai an tabbatar da gaskiyar abin da ake bincike.

Idan za’a iya tunawa TST Hausa ta rawaito cewa a yayin karbar kudirin sa dan majalisar dokokin Kano daga Karamar hukumar Dambatta Hon.Murtala Musa Kore ya gabatar ,an ambaci sunan shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB), Yusuf Kabir, a matsayin daya daga cikin jami’an da ya kamata suje majalisar su bada bayanin abinda ya faru kan zargin badakala a daukar aikin na malaman makaranta.

Saidai Hon.Shehu Isa Direba ya shaida cewa a matsayin shugaban na SUBEB da ke da kima da tarihin aiki mai kyau, kamata yayi a gudunar da binciken cikin sirri domin yi masa adalci saboda gudun kada gano bashida laifi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version