Majalisar dokokin Jihar Kano ta gayyaci Shugaban hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Yusuf Kabir (SUBEB), domin bayar da bayani kan yadda aka gudanar da aikin daukar ma’aikata a hukumar, biyo bayan korafe-korafe da rashin gamsuwa da tsarin da aka bi.

TST Hausa ta rawaito cewa ana zargin wasu sunyi amfani da kudi wajen sayan takardar daukar aikin koyarwa da gwamnan jihar Kano ya bada umarni aka dauka sama da mutane dubu 7.

Wani bincike ya gano cewa a kalla kaso 90 cikin 100 na mutanan da suka nemi aikin sayan takardar sukayi da kudi.

Gayyatar shugaban na SUBEB ya biyo bayan gabatar da kudirin nuna rashin amincewa a zauren majalisar daga ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dambatta, Murtala Musa Kore, wanda ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da sake duba yadda aka aiwatar da daukar ma’aikata aikin koyarwa.

Majalisar ta bayyana cewa tana da burin tabbatar da adalci, gaskiya da bin ka’ida a dukkan matakan daukar ma’aikata, domin kauce wa nuna son kai da kuma tabbatar da ingancin harkar ilimi a jihar.

Ana sa ran shugaban na SUBEB zai gurfana a gaban majalisar domin karin haske kan lamarin da ake takaddama a kai.

Da yiyuwar a soke daukar aikin da akayi saboda zargin cin hanci da rashawa

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version