Karamar hukumar Bichi a Kano ta karbi daruruwan baki daga Sassan Najeriya domin shaida yadda aka ɗaura auren Bashir Kabiru Ado Minjibir da amaryarsa Halima Garba Usman, a wani gagarumin biki da ya haɗa shugabannin ƙwadago, masu fafutukar kare haƙƙin jama’a, sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati.

An daura auren ne a babban Masallacin juma’a na garin Bichi.

Naira dubu dari Biyu (200,000) shine kudin sadakin da Ango Bashir ya biya.

Daurin Auren ya samu halartar shugabannin Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da na jihohi daban-daban, waɗanda suka yi tururuwa zuwa Bichi domin taya jagoransu, Kabiru Ado Minjibir, murnar auren babban ɗansa da ya aurar na farko.

Fitattun ‘yan gwagwarmayar daga sassa daban-daban na Najeriya da suka halarci taron sun shaidawa TST Hausa cewa zuwansu wata alama ce ta girmamawa da kuma nuna irin matsayin da Kabiru Ado Minjibir ya samu a fagen gwagwarmayar kare haƙƙin ma’aikata da ci gaban al’umma a Najeriya.

A madadin Gwamnan Jihar Kano, Mataimakin Gwamna,Alhaji Murtala Sule Garo ya halarci bikin tare da isar da saƙon taya murna daga gwamnatin jihar.

Haka shima Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kasance cikin manyan baƙin da suka halarta.

Taron shaida Auren ya kuma samu halartar shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya, shugabannin ƙungiyoyin sa-kai, tare da Hakimai da Dagatai daga sassa daban-daban, lamarin da ya ƙara wa taron armashi da kima.

Kabiru Ado Minjibir, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), kuma Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya, sannan Magayakin Minjibir, ya karɓi baƙi cikin karamci da girmamawa, yayin da jama’a suka yaba da irin kyakkyawar alaƙar da ya gina tsawon shekaru da ma’aikata,da shugabanni da al’umma baki ɗaya.

Masu halartar bikin sun bayyana cewa taron ba kawai bikin aure ba ne, har ila yau ya zama wani babban dandali na haɗa kan al’umma, ƙarfafa zumunci da kuma sake tabbatar da haɗin kan shugabannin ƙwadago, masu fafutuka da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

An gudanar da bikin cikin walwala da annashuwa, inda aka yi addu’o’in neman albarka ga sabbin ma’auratan, Bashir Kabiru Ado Minjibir da Halima Garba Usman, tare da fatan Allah Ya ba su zaman lafiya, soyayya mai ɗorewa, zuri’a ta gari da albarkar rayuwar aure.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version