Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu a Asibiti a London bayan gajeruwar rashin lafiya.

Tsohon hadiminsa akan kafofin yada labarai Bashir Ahamad shine ya sanar da hakan a shafinsa na sada zumunta Inda yace iyalansa ne suka sanar da mutuwar sa.

Ya rasu yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.

An haifeshi a ranar 17 ga watan  Disamba na shekarar 1942 ya koma ga Allah ranar 13 ga watan Yuli na 2025.

Ya mulki Najeriya a zamanin mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1985.

Daga nan ya koma mulkin farar hula a shekarar 2015 zuwa 2023.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version