Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikicin  siyasa da jihar ta fada tsawon lokaci.

Shugaban ya ayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a kan matsalar siyasar da ke addabar jihar ta Rivers.

Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna a tsawon lokaci.

Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na sashi na 305 na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025

An dakatar da gwamnan Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa na tsawon wata shida.

Tinubu yace yayi iyakar bakin kokarinsa kan yadda za a magance matsalar to amma duka bangarorin sun yi watsi da yunkurin nasa

Haka nan shugaban ƙasa ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma babu mafita.

A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Rivers.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version