Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya jaddada cewa ba zai taɓa amincewa da duk wani shiri ko haɗin kai da zai iya janyo cutarwa ga alhazan jihar Kano ba, yana mai tabbatar da hakan tare da rantsuwa da Allah Madaukakin Sarki.

Matawalle ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da sabbin kwamitoci da zasu jagoranci aikin Hajjin Bana a kasa mai tsarki.

TST Hausa ta rawaito cewa kwamitocin da Alhaji Matawallen ya kaddamar sun kai guda 8.

Kwamitocin sun hada da na yada labarai da likitoci da Muhalli da Sharia da Hisba da yada labaran yanar gizo da na fadakarwa da masu kula da masauki da sauransu.

Ya ce, “Ba zan taɓa haɗa kai da kowa ba domin cutar da alhazan Kano, duk abinda yake kan doka shi zanyi ” In Ji Matawalle.

Yace “wannan aiki amanar jama’a ce, kuma dole ne mu sauke nauyin da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dora mana aka ɗora mana”, In ji shugaban.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa, sun ɗauki matakai daban-daban domin tabbatar da jin daɗi,da tsaro da walwalar alhazai tun daga shirye-shiryen tafiya har zuwa lokacin da za su kammala ibadarsu su dawo gida lafiya.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin da suka dace domin inganta harkokin hajji, tare da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo tangarda ga tafiyar alhazai.

A ƙarshe, Matawalle ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da jita-jita marasa tushe, su kuma bai wa hukumar cikakken goyon baya domin samun nasarar gudanar da aikin hajji cikin tsari da nasara.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version