Hukumar Kula da Masallacin Harami da Masallacin Annabi SAW ta bayyana cewa ana fitar da sama da lita miliyan 1.6 na ruwan Zamzam a kowacce rana domin wadatar da l mahajjata sama da miliyan 1 da dubu dari 7 a lokacin aikin Hajjin bana.
A cewar hukumar, yawan amfani da ruwan Zamzam kan kai kusan lita miliyan 2 a rana a lokutan da ake samun cunkoson mahajjata, musamman a kwanakin da ake gudanar da muhimman ibadun Hajji.
Hukumar ta ce ta samar da cikakken tsarin rarraba ruwan Zamzam a cikin Masallacin Harami da sauran wuraren da mahajjata ke gudanar da ibadunsu, tare da tanadin dubban tankuna da na’urorin sanyaya ruwa domin tabbatar da cewa kowa ya samu ruwan cikin sauƙi.
Ta ƙara da cewa ana amfani da fasahohin zamani wajen tacewa,da adanawa da kuma kula da ingancin ruwan Zamzam, domin tabbatar da cewa yana isa ga mahajjata cikin tsafta da aminci.
Hukumar ta bayyana cewa wadatar ruwan Zamzam na daga cikin manyan hidimomin da Masarautar Saudiyya ke bayarwa ga baƙin Allah, tare da jaddada ƙudirinta na ci gaba da inganta ayyukan da ke taimakawa mahajjata wajen gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali.
Ruwan Zamzam na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ni’imomin da mahajjata ke amfana da su a ƙasa mai tsarki, inda miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya ke shansa tare da ɗaukar sa zuwa ƙasashensu bayan kammala aikin Hajji.
