Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa har yanzu bai yanke wata ƙarsasshiyar shawara ba dangane da makomarsa ta siyasa, duk da rade-radin da ke yawo kan yiwuwar sauyin sheƙa a cikin jam’iyyar ADC.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce rahotannin da ke nuna cewa ya riga ya yanke hukunci kan makomarsa ko ta abokan tafiyarsa ba su da tushe.

Ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke kwanan nan, wanda ya tabbatar da sahihancin shugabancin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin David Mark, ya kuma mayar da batun zuwa babbar kotu, ya jefa jam’iyyar ADC cikin wani yanayi mai rikitarwa.

Haka kuma, ya bayyana cewa babbar kotun tarayya ta soke sahihancin babban taron jam’iyyar na baya-bayan nan, yayin da ministan Sharia ya nemi a soke rajistar jam’iyyar gaba ɗaya.

Kwankwaso ya ƙara da cewa sun fice daga jam’iyyar NNPP ne sakamakon matsalolin shari’a da suka taso daga waje, waɗanda suka sanya ci gaba da kasancewa a cikinta ya zama haɗari, yana mai cewa irin wannan matsala ce yanzu ADC ke fuskanta.

Ya ce tare da sauran manyan ’yan siyasa, sun fara tuntuba da shugabannin wasu jam’iyyu kamar (NDC) da PRP domin nemo mafita mafi dacewa.

Dangane da rade-radin tsayawa takarar shugaban ƙasa, Kwankwaso ya jaddada cewa bai bayyana aniyarsa ba, kuma bai mara wa kowa baya ba, yana mai cewa jam’iyyar ADC ma har yanzu ba ta yanke hukunci kan tikitin shugaban ƙasa ba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version