Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta fara karɓar kuɗin ajiye kujerar aikin Hajjin shekarar 2027, inda ta kayyade adadin kuɗin a matsayin Naira miliyan takwas (₦8,000,000) ga kowane maniyyaci.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar,ta hannun mai magana da yawunta Malam Sulaiman Ibrahim Dederi ya bayyana cewa za a fara karɓar kuɗin daga ranar Lahadi, 12 ga Yuli, 2026, sannan za a rufe karɓar kuɗin a ranar 26 ga Satumba, 2026.

Hukumar ta buƙaci duk masu niyyar gudanar da aikin Hajjin 2027 da su gaggauta biyan kuɗin ajiya ta hanyoyin da aka amince da su, domin tabbatar da samun gurbi cikin lokaci da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen aikin Hajji.

Haka kuma, ta shawarci maniyyata da su guji jira zuwa ƙarshen wa’adin biyan kuɗin, domin kauce wa cunkoso da duk wata matsala da ka iya tasowa yayin gudanar da rajista.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version