Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, Abdullahi Gali Shitu Bassaf, ya koma sana’ar ɗinki da yake yi tun kafin shiga siyasa, bayan kammala wa’adinsa na shugabancin ƙaramar hukuma.
Shitu ya bayyana cewa komawarsa sana’ar tasa na nuna cewa riƙe muƙamin gwamnati ba ya hana mutum ci gaba da gudanar da halastacciyar sana’arsa.
Ya ce sana’a ita ce ginshiƙin dogaro da kai, kuma tana tabbatar da cewa mutum na iya ci gaba da rayuwa cikin mutunci ko da bayan barin ofis.
Ya kuma yi kira ga matasa da kada su dogara da neman muƙaman gwamnati ko aikin gwamnati kaɗai, yana mai jaddada muhimmancin koyon sana’o’in hannu domin samar da abin dogaro da kai da rage rashin aikin yi.
A cewarsa, gwamnati da masu ruwa da tsaki su ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen koyar da sana’o’i da ƙarfafa matasa su rungumi aikin yi, domin hakan na da matuƙar tasiri wajen bunƙasa tattalin arziki da rage talauci.
Matakin da tsohon shugaban ƙaramar hukumar ya ɗauka ya jawo martani daga jama’a da dama, inda wasu ke yabawa da cewa ya zama abin koyi ga masu riƙe da muƙaman gwamnati, tare da nuna cewa babu aibu a komawa sana’ar da mutum ya gada ko ya koya bayan kammala hidimar jama’a.
