A yayinda watan Azumin Ramadan ke karewa ,a wannan rana ta Juma’a da ta kasance ta karshe a watan Ramadan na bana, dandazon Musulmi daga sassa daban-daban na duniya sun hallara a Masallacin al‑Haram dake birnin Makkah, domin gudanar da Sallar Juma’a ta karshe a watan mai alfarma.
Sheikh Faisal bin Jameel bin Hasan Al‑Ghazzawi, limamin masallacin, shi ne ya jagoranci sallar.
A cikin hudubarsa, ya yi doguwar addu’a ga Allah, inda ya roƙi Allah ya maimaita Ramadan ga Musulmai a shekara mai zuwa, sannan ya karɓi dukkan ibadun bayinsa da aka yi a wannan watan mai alfarma.
Sheikh Ghazzawi ya ja hankalin jama’a cewa, har yanzu akwai damar neman gafara da dacewa a wannan watan, yana ƙarfafa Musulmai su ci gaba da yin ibada, addu’a da kyawawan ayyuka kafin ƙarshen Ramadan.
Bugu da ƙari, Sheikh Ghazzawi ya ja hankalin jama’a kan muhimmancin neman Daren Lailatul Qadar musamman idan bai wuce ba a kwanakin baya yana ƙarfafa Musulmai su yi adu’a,da ibada da kyawawan ayyuka a kwanaki na ƙarshe na Ramadan, domin samun gafara da lada mai yawa.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/hudubamatasan-yanzu-idon-su-ya-rufe-da-neman-kudi-shiyasa-suke-saka-kansu-a-caca-da-crypto-dr-abdullah-gadon-kaya/
TST Hausa ta rawaito cewa Jama’a sun nuna farin ciki da natsuwa yayin da limamin ke jagorantar sallar da karatun Al‑Qur’ani cikin ladabi duk da zafin rana da aka samu a wannan rana
Wannan sallar ta karshe ta zama wata muhimmiyar dama ga Musulmai domin roƙon gafara, karɓar ibada da samun lada, inda aka ji dadin haɗin kai da tsantsar imani tsakanin jama’a.
