Amirul Hajj na Jihar Kano kuma Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya bukaci dukkan jami’ai da kwamitocin da aka dorawa nauyin gudanar da aikin Hajjin 2026 da su kara zage damtse tare da aiki cikin hadin kai domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana

Shugaban kwamatin tawagar yan Jarida dake kula da harkokin yadda aikin Hajji ke gudana Alhaji Mustapha Muhammad ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya fitar inda yace Sarkin ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na dabarun gudanar da aiki da aka gudanar a House Number One da ke birnin Makkah a ranar Lahadi, inda ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, biyayya ga aiki da kuma fahimtar juna tsakanin dukkan bangarorin da ke gudanar da aikin Hajjin

Ya ce nasarar aikin Hajji ba za ta samu ba sai an hada kai tare da nuna kwarewa da jajircewa wajen kula da alhazai da gudanar da ayyukan da aka tsara.

Don haka ya bukaci jami’an da su kasance masu aiki tukuru tare da fifita bukatun alhazai a duk lokacin gudanar da aikin.

“Hadin kai da aiki tare su ne ginshikin nasarar duk wani aiki, musamman aikin Hajji wanda ke bukatar tsari, hakuri da cikakken kulawa,” in ji Amirul Hajjin.

Da yake nasa jawabin, Mataimakin Amirul Hajj kuma Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Mahraz Karaye, ya bayyana cewa shugabannin tawagar Hajjin Kano sun kuduri aniyar ganin an gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsari da nasara.

Ya ce shirye-shiryen Mina da Arafat na daga cikin muhimman matakan aikin Hajji, kasancewar su ne ginshikin dukkan ayyukan da ake gudanarwa a lokacin aikin Hajjin. Saboda haka ya bukaci dukkan kwamitoci da su kara hada kai tare da taimaka wa juna domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Hakazalika, ya umarci dukkan kwamitoci da su tattara rahotanninsu bayan kammala zaman Arafat domin hada cikakken rahoton aikin Hajjin 2026.

A nasu bangaren, shugabannin kwamitoci daban-daban sun tabbatar wa shugabannin Amirul Hajj cewa suna nan a shirye domin yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana ga alhazan Jihar Kano

Taron ya kare ne cikin yanayi na fahimtar juna da sabunta alkawarin aiki tare tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin kwanciyar hankali da nasara.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version