Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta fara aikin kwato motocin gwamnati da ke hannun wasu tsofaffin jami’an gwamnatin jihar, bayan zargin kin mayar da su duk da kammala wa’adin aikinsu.

Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ne ya jagoranci aikin a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026.

Ya bayyana cewa tun da fari Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya aika da wasiƙu ga tsofaffin jami’an da abin ya shafa, inda aka umarce su da su mayar da motocin gwamnati da ke hannunsu.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-na-da-yancin-barin-nnpp-zuwa-apc-kamar-yadda-kwankwaso-ya-bar-pdp-zuwa-nnpp-shekarau/

Sai dai, a cewarsa, wasu daga cikinsu ba su bi wannan umarni ba, lamarin da ya sa hukumar ta ɗauki matakin kwato motocin domin kare dukiyar al’umma da tabbatar da bin doka da oda.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/%c9%97ana-ya-shiga-apc-ne-bisa-radin-kansa-atiku/

Daga cikin tsofaffin kwamishinonin da aka kwato motocin a hannunsu akwai tsohon Kwamishinan Tsaro, Ibrahim Umar; tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabiu Kwankwaso; tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Yusuf Ibrahim Kofar Mata; tsohon Kwamishinan Jin Kai, Adamu Aliyu Kibiya; da kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo.

Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da doka ta tanada wajen kare kadarorin gwamnati, tare da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin tafiyar da mulki a Jihar Kano.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version