Gwamnan Jihar Kano,Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin a yanka ragon lauya ga wasu ƙananan yara da ya hadu da su a makabarta Goron Dutse.
Lamarin ya faru ne yayin da gwamnan ya kai ziyara zuwa makabartar,domin yin Adu’a ga marigayi Mahaifinsa Alhaji Kabir Yusuf inda ya ci karo da wasu yara ƙanana da suka haɗa da Saddika Kabiru Baba da Amaturrrahaman, mazauna unguwar Alfindiki.
TST Hausa ta rawaito cewa yaran sunje ne domin yin adua ga kakanninsu da suka rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa ganin yaran ya sanya gwamnan nuna tausayi da kulawa, lamarin da ya sa ya bayar da umarnin a yanka ragon domin yi musu layya bayan ya tambayesu akan ko anyi musu layar, suka amsa da a’a.
Mahaifin yaran Kabiru Labaran Baba shine ya tabbatarwa da TST Hausa abinda ya faru a kasa mai tsarki.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin,babban sakataren Yaɗa Labaran gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya ce matakin wani ɓangare ne na halayen tausayi da kulawar Gwamna Abba Kabir Yusuf ga marasa galihu da ƙananan yara.
Ya bayyana cewa gwamnan ya kan nuna damuwa da jin ƙai ga al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi, yana mai cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa mabukata a faɗin jihar.
Matakin na Abba Kabir Yusuf ya jawo yabawa daga jama’a, inda wasu suka bayyana hakan a matsayin abin koyi na shugabanci mai tausayi da kusanci da talakawa.
