Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da rufe ƙofofin shiga wajen Jifan Shaidan wato Jamarat bayan kammala Hajjin bana, lamarin da ke nuna kawo ƙarshen amfani da wurin domin tunkarar ibadun Hajji na shekarar 1448 Hijira daidai da 2027.

Matakin ya biyo bayan kammala jifa da Alhazai suka yi a ranakun Tashrīƙ, inda miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya suka gudanar da ibadar cikin tsari, aminci da kwanciyar hankali.

Jamarat na daga cikin muhimman wuraren da Alhazai ke ziyarta a Mina domin gudanar da ibadar jifar shaidan, wadda ke daga cikin manyan rukunan ayyukan Hajji.

Rufe ƙofofin wurin na nufin an kawo ƙarshen zirga-zirgar Alhazai zuwa Jamarat a bana, yayin da hukumomin Saudiyya za su fara shirye-shiryen kula da wurin da kuma tunkarar aikin Hajjin shekara mai zuwa.

A bana, an gudanar da ayyukan Hajji cikin nasara, inda hukumomin Saudiyya suka samar da tsare-tsaren tsaro, lafiya da sufuri da suka taimaka wajen sauƙaƙa gudanar da ibadun miliyoyin Alhazai da suka halarci aikin Hajjin bana.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version