Wata babbar kotun majistire a Kano ta bayar da umarni ga ‘yan sanda su gudanar da cikakken bincike kan zargin batanci da ake yi wa mai jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar.

Alkalin kotun, Malam Abdul’aziz M. Habib na kotu mai lamba 15 dake Nomansland, ya saurari karar da Darakta Janar na Sashen Huldar Diplomasiyya na Fadar Gwamnatin Kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar.

Rogo ya gurfanar da Jafar tare da wani Audu Umar bisa zargin bata masa suna, inda aka wallafa shi a matsayin “thieving aide” wato “hadimin barawo” na Gwamna Abba Kabir Yusuf a wasu rahotannin da Daily Nigerian ta wallafa a ranar 22 da 25 ga watan Agusta, 2025.

A cikin karar da aka shigar a ranar 28 ga watan Agusta, 2025, DG Protocol ya ce rahotannin guda biyu da suka ce:

A ranar R 25 ga Agusta Jafar Jafar ya buga Labarin cewa Gwamna Yusuf ya kare barawon da ake zargi da sata

Sannan a ranar 22 ga Agusta Jafar Jafar ya buga Labarin cewa daraktan tsare tsare na ofishin gwamnan jihar Kano Abdullahi Rogo ya karkatar da kuɗi naira miliyan dubu 5 da rabi.

Inda gwamnatin tace duka ƙarya ne da aka yi da niyyar bata masa suna da na gwamnan jihar.

Karar ta dogara ne da sashe na 106 da 107 na dokar shari’ar laifuka ta Kano (2019), da kuma sashe na 114, 164 da 393 na kundin Penal Code, inda ake neman a gurfanar da su bisa laifin batanci da kuma take hakkin zaman lafiya.

Alkalin kotun ya bayar da umarni ga mataimakin babban sifeton yan sanda shiya ta daya  AIG dake Kano da ya gudanar da bincike mai zurfi kan rahotannin da aka wallafa.

An sanya hannu a kan umarnin ta hannun rajistar kotu a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2025.

A gefe guda kuma, an kuma shigar da wani kara ta farar hula a gaban babbar kotun jihar Kano, inda Rogo ke neman diyya kan batanci daga Jafar Jafar da jaridar Daily Nigerian.

Gwamnatin Kano ta riga ta nesanta kanta daga zargin satar kudin N6.5 biliyan, inda ta ce labarin “ƙirƙira ne na abokan adawa da suka maida siyasa hanyar batanci da farfaganda.”

Yanzu dai kotu ta umarci ‘yan sanda da su binciki dalilin da yasa Jafar ya saba ƙa’idar aikin jarida da kuma kiran jami’in gwamnati da “barawo” alhali kuwa hukumar ICPC tana kan bincike a kansa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version